
A ranar ta biyu a shari'ar da ake yi game da zargin
kisan da ake wa Oscar Pistorius, kotu za ta cigaba da sauraron bayanai
daga masu shigar da kara.
Ana tuhumar zakaran wasan tseren nakasassun ne
da harbin budurwar sa, Reeva Steenkamp lamarin da ya yi sanadiyar
mutuwar ta, a makon jiya.Ana sa ran jin bayanai da za su karyata wadanda Mista Pistorius ya gabatar a ranar farko.
Shi dai Pistorius ya musanta cewa ya kashe budurwarsa, wacce aka harbe a gidansa ranar Alhamis.
A wata sanarwa da ya fitar, ya ce ya yi tsammanin barawo ya kashe a lokacin da ya yi harbin.
Sai dai a zaman farko da kotun ta yi, mai shari'ar ta ce za ta saurari karar ne a matsayin wadda aka yi kisan kai da gangan.
Kotun wacce ke birnin Pretoria za ta saurari bukatar yiwuwar ba da belin Mista Pistorius, a rana ta biyu da ake gudanar da sharia a kansa.
Dan wasan dai ya musanta zargin da ake yi masa.
No comments:
Post a Comment