
Gwamnatin jihar Nasarawa a arewacin Najeriya ta bada
umarnin rufe jami'ar jihar dake garin Keffi bayan wata mummunar
zanga-zanga da ɗalibai suka yi suna nuna rashin jin daɗinsu da matsalar
karancin ruwa da suke fuskanta.
A lokacin zanga-zangar daliban sun toshe babban titin da ke zuwa Abuja, inda suka ƙona tayoyi.Daga bisani kuma an tura jami'an tsaro domin tarwatsasu.
Rahotanni sunce an samu asarar rayuka bayan da jami'an tsaro suka isa wurin masu zanga zangar.
Ɗaliban dai sun ce sun yi zanga-zangar ce saboda mummunan Ƙarancin ruwan da suke fama da shi.
No comments:
Post a Comment