Friday, 15 February 2013

Kwararru za su gana game da naman doki

 

A ranar Juma'a ne kwararru kan harkar kula da ingancin abinci a nahiyar Turai za su gudanar da taro a Brussels don tattaunawa kan badakalar nan ta sayar da naman doki a matsayin naman shanu.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan sanda a Burtaniya suka kama mutane uku da ake zargi da hannu da sayar da naman doki a matsayin naman shanu.
Tun da farko hukumomin kasar Faransa sun soke lasisin wani kamfanin kasar da ake zargi da sayar da fiye da tan dari bakwai na naman doki a matsayin naman shanu.
Sai dai Kamfanin mai suna, Spanghero, ya musanta zargin.
Wadansu manyan shaguna a kasar Jamus sun fara janye naman shanun da ake sayarwa a shagunansu.

No comments:

Post a Comment