
Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno
na cewa, akalla mutane takwas ne su ka mutu sanadiyar fashewar wani abu
da ake kyautata zaton bam ne a unguwar kwastan.
Bakin hayaki ya turnike sararin samania kamar
yadda shaidun gani da iddo su ka tabbatar, tare da cewa Shaguna da dama
da su ka kone.Wasu magidanta a Maidugurin sun tabbatar wa da cewa sun ga gawawwakin mutane a kwance.
Wannan al'amari dai ya kara janyo zaman zulumi a birnin.
Ko a ranar laraba ma dai, wasu mutane uku sun mutu bayan fashewar wani abu a birnin Maidugurin.
No comments:
Post a Comment