Friday, 15 February 2013

An zargi shirin rediyo da jaza kasan ma’aikatan allurar Foliyo

 


A ranar Talatar da ta gabata ne aka gurfanar da tsohon Darakata Janar din Hukumar Tace Fiian-finai ta Jihar Kano,  Malam Rabo Abdulkarim da ‘yan jarida da ke aiki da gidan rediyon Wazobiya wadanda suka hada da Yakubu Musa Fagge da Mubarak Sani Muhammad
, a gaban wata kotun majistare mai lamba 17 da ke unguwar Gyadi-gyadi cikin Jihar Kano bisa zarginsu da laifin hadin baki bisa tunzura jam’a  su kyamaci allurar rigakafin shan inna tare da cin zarafin Hakimin Tarauni dan goribar Kano a cikin shirin gidan rediyon wazobiya na ‘Sandar Girma.’
Tunda farko mai gabatar da kara Sajan Sadik Na’abba  a cikin takardar karar da ya karanta a gaban kotun ya bayyana cewa,. “Kai Malam Rabo Abdulkarim wanda ke zaune a gida mai lamba 155 a kan titin Maiduguri a karamar Hukumar Tarauni ka bijire wa ma’aikatan allurar rigakafin shan inna inda ka nuna ba za su yi wa ‘yayanka ba. Hakan ya jawo Hakimin Taruni da sauran shugabnnin da ke kula da aikin allurar suka je gidanka don sanin dalilinka na kyamar allurar. Amma sai aka samu ka hada baki da wadansu ‘yan jarida da ke aiki a gidan rediyon Wazobiya inda suka gabatar da wani shiri na ‘ Sandar Girma’  don tunzura jama’a su kyamaci allurar Foliyo din tare da cin mutuncin Hakimin Tarauni. Har ila yau kuma hakan shi ya yi sanadiyar da aka kai wani hari har aka kashe wasu ma’aikatan foliyo a kanan hukumomin Tarauni da kuma Nassarawa wanda hakan laifi ne da ya saba wa sashe na 97 da 85 da 399 da 392 da 393 na kundin laifuka na Finalkod (pinal code).
Sai dai dukkanin wadanda ake zargin sun musanta laifin da ake zargin su da shi.
Mai shari’a Bello Ibrahim ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 14 ga wannan watan don ci gaba da sauraran shari’ar, tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare wadanda ake zargi har zuwa ranar da za a ci gaba da saurarn shari’ar.
Rundunar  ‘yan sandan Jihar Kano dai ta kama ‘yan jarida wadanda ke aiki da gidan rediyon Wazobiya FM da kuma tsohon Darakta Janar na Hukumar tace Fina-finai ta Jihar Kano, Malam Rabo Abdulkarim ne inda take bincikensu game da wani shiri da gidan rediyon ya watsa a makon da ya gabata a game da cutar foliyo.
‘Yan jaridar da ‘yan sandan suka kame sun hada da Shugaban sashin shirye-shirye na gidan rediyon Wazobiya Muhammad Sulaimanu Gama da kuma maishiryin wani shiri mai suna ‘’Sandar girma’’ Yakubu Musa Fagge da kuma  mai dauko rahoto, Mubarak Muhammad Sani.
Shugaban gidan rediyon na Wazobiya Malam Sanusi Bello Kankarofi ya bayyana wa Aminiya cewa, a ranar Lahadin da ta gabata ne rundunar  ‘yan sandan ta gayyaci ma’aikatansu guda uku  don bincike.  “Tun daga wancan rana kuma aka tsare ma’aikatan namu ba tare da wani dalili ba. Mun nemi su sanar da mu wane shiri ne muka sanya a rediyo wanda har ya jawo aka aiwatar da hari a kan ‘yan sandan da ke yi wa ma’aikatan alluar rigakafin cutar shan inna rakiya, amam sun kasa ba mu amsa. Mu muna ganin ana so a yi amfani da wannan dama ne a wulakanta ‘yan jarida saboda wani dalili na siyasa.” Inji shi.
Sai dai a hirar da ya yi da manema labarai, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano Alhaji Ibrahim K. Idris ya musanta wannan zargi, inda ya ce, “Babu shakka mun kama wadannan mutane, sai dai ba mu kama su a matsayinsu na ‘yan jarida ba, sai don gudanar da wani bincike da muke yi. Da zarar mun kammala bincikenmu za mu sanar da jama’a halin da ake ciki.” Inji shi.
Aminiya ta samu damar tattaunawa da Malam Rabo Abdulkarim a lokacin da yake tsare, inda ya bayyana wannan kame a matsayin cin zarafin bil’Adama, “Tun da dai mun san a kan gaskiya muke to muna yi wa Allah godiya. Babban fatanmu shi ne game da wannan ma’amala ta allurar rigakafin shan inna a daina tursasa talakawa a kai, ba wai a kan wannan kawai ba, dukkanin wadansu abubuwa da aka kawo komai kyawunsu bai kamata a turasasa jama’a a kai ba. Abin da ya kamata a yi shi ne a yi kokarin ilimantar da jam’ar har su gane alfanun da ke cikin lamarin. Yadda mutne za su rika yin mua’amala kowace iri ce bisa ra’aiyin kansu da kuma bisa ilimantar da su da aka yi.”
Shi ma a nasa bangaren, mai gabatar da shirin na ‘Sandar Girma’  Yakubu Musa Fagge ya bayyana cewa babu wani abu na hadin baki tsakanin gidan rediyonsu da Malam Rabo wajen aikewa da ma’aikacinsu, haka kuma ba shirinsa na Sanda ne ya jawo aka kai hari kan ma’aikatan foliyo ba. “Gaba daya dai laifin da ake tuhumarmu da shi, shi ne mun hada baki da Malam Rabo wajen aika wakilinmu don ya dauki rahoton  takaddamar da za ta faru tsakaninsa da masu allurar shan inna. Hakan ya sa na ba wa ‘yan sandan hujjoji guda uku wadanda suka karyata hakan, sai dai sun ce har yanzu suna nan suna gudanar da bincike. Haka kuma shirinmu na Sanda ba shi ne ya jawo aka kai hari a kan ma’aikatan foliyo ba.” Inji Yakubu.
Aminiya ta samu zantawa da Shugaban sashin shirye-shirye na gidan Rediyon Wazobiya Muhamamd Sulaiman Gama jim kadan bayan an bayar da belinsa, ya bayyana wa Aminiya cewa duk da cewa ba a gaya musu laifin nasu kai tsaye ba, amma an sanar da su cewa shirinsu na Sanda shi ne ya tunzura jama’a kyamatar allurar rigakafi, haka kuma shirin ne ya jawo ‘yan bindiga suka kai hari a kan ma’aikatan foliyo. “Rigimar ta fara ne bayan an doki ma’aikacinmu a lokacin da ya dauki rahoto a kan rigimar rigakafin allurar  tsakanin Malam Rabo da tawagar masu tabbatar da cewa an yi allurar har aka kwace masa kayan aikinsa, hakan ya sanya mai gabatar da shirin Sanda ya tabo waccan magana a cikin shirinsa wacce kuma ba ta yi musu dadi ba. Haka kuma sai ga shi washegri an kai hari kan masu allurar rigakafin har aka kashe mutum tara a cikinsu. Wannan ne ya sa aka ce ana tuhumar ma’aikatanmu.” Inji shi.
Binciken Aminiya ya gano cewa ‘yan sanda suna kokarin hada alaka tsakanin shirin da gidan rediyon Wazobiya ya gabatar da kuma harin da aka kai washegari kan ma’aikatan foliyo a jihar, inda suke zargin shirin na sanda da hura wuta tare da tunzura jama’a kyamar allurar polio.
Idan za a iya tunawa a ranar Talata biyar ga watan Fabreru  dan jarida da ke aiki da gidan rediyon Wazobiya ya sha da kyar sakamakon dukan da wadansu matasa suka yi masa a daidia lokacin da yake gudanar da aikinsa.
Kamar yadda dan jaridar da ya sha dukan mai suna Mubarak Muhammad Sani ya bayyana wa Aminiya, ya ce a daidai lokacin da yake hira da tsohon Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Malam Rabo Abdulkarim a gidansa a kan wani lamari daban, sai ga tawagar da ke lura da allurar rigakafin sun shigo gidan wadanda suke son ganin Malam Rabo a kan wata magana ta daban. “Lokacin da muke tattunawa da Malam Rabo sai tawagar masu allurar rigakafin, da ta kunshi Shugaban Riko na karamar Hukumar Tarauni da Hakimin Tarauni da kuma wadansu ‘yan bangar siyasa,da wanda na ke zaton ‘yan jam’iyyar PDP ne, domin dukkaninsu suna sanye da jajayen huluna, sai suka shigo gidan inda suka nemi mu dakatar da abin da muke yi har sai sun gama abin da ya kawo su gidan. A lokacin da na fuskanci tirka-tirka da mujadala ta kaure a tsakaninsu sai na fara daukar labarin. Yayin da suka fuskanci abin da nake yi  sai Hakimi ya ba wa matasan nan umarni da  su fitar da ni waje tare da duka na.”
dan jaridar ya kara da cewa, “Na yi kokari  wajen fahimtar da su abin da ya faru amma suka ki saurara ta, inda suka yi kwallo da ni zuwa waje, suka yi min duka, ta hanyar hada hannayensu bibbyu suka rika dukana a fuskata da gefen kunnuwana. Saboda tsananin duka wallahi kasa gane abin da yake faruwa na yi. Sai na rika jin wani dum a kaina.”
Malam Mubarak wanda yake kwance a gida yake jinyar raunikan da ya samu a lokacin wanann waki’a, ya bayyana cewa, tawagar ta kwace wayarsa da rediyon daukar maganarsa  tafi da su, sai da shugabanninsa suka sanya baki sannan aka dawo masa  da kayayyakinsa.
A lokacin da Aminiya ta tuntubi mai taimaka wa Gwamnan Kano a kan harkokin watsa labarai, Ja’afar Ja’afar ya musanta faruwar wannan lamari, inda ya ce babu wani mutum mai halkali da zai sa a doki wani, ballanatan kuma bababn mutum kamar Hakimi. “Wanann magana babu gaskiya a cikinta. Ta yaya ma babbn mutum kamar Hakimi zai sa a doki dan jarida. Ban da ma haka yaya za a yi a tabbatar da cewa mutanen da suka yi dukan ‘yan PDP ne don kawai sun sanya jar hula? Kowa ma zai iya sanya jar hula ya badda kama a matsayin dan jam’iyyar PDP.” inji Ja’afar.
A washegarin ranar  Laraba ne a cikin shirin Sandar Girma gidan rediyon Wazobiya ya bayar da rahoto game da dukan kawo wuka da aka yi wa wakilinsu a lokacin da yake gudanar da aikinsa na daukar rahoto a kan tirka-tirkar da ke faruwa game da allurar rigakafin cutar shan inna.  An ce dai wanann shiri ne ya ja musu jangwam inda ake zarginsu da laifin tunzura jama’a bisa kyamar allurar rigakafin.

No comments:

Post a Comment