Kotun manyan laifuka ta duniya ta bukaci Kasashen
Chadi da Libya da su tsare Shugaba Omar al Bashir na Sudan, sannan a
tusa keyarsa domin ya fuskanci shari'a, idan har ya ziyarci Kasashen
biyu a karshen mako
Wannan umarni shine yunkurin Kotun dake Hague na baya bayan nan na ganin cewa an tsare shugabanAna dai zargin sa da shirya kisan kare dangi da kuma aikata laifukan yaki a yankin Darfur na Sudan
Kasashen Chadi da Kenya da wasu kasashen Afirka da dama sun karbi bakwancin Mr Bashir, duk da cewa dukkanin su sun amince da kotun manyan laifukan
No comments:
Post a Comment