
A ranar Juma'a za a gurfanar da zakaran tseren
nakasassu na Afrika ta Kudu, Oscar Pistorius, a gaban kuliya saboda
zargin da ake yi masa na kashe budurwarsa a gidansa da ke Pretoria.
An harbi Reeva Steenkamp sau hudu a kanta da wadansu sassan jikinta ranar Alhamis.Ba ta dade ba ta mutu.
'Yan sanda sun ce sun samu wata karamar bindiga a wajen da ta mutu.
Tun da farko 'yan sanda sun yi wa Mista Pistorius tambayoyi.
Daga bisani an kai shi wani asibiti domin gwada jininsa.
No comments:
Post a Comment