Tuesday, 19 February 2013

Pistorius ya 'harbe budurwarsa a bandaki

 Oscar Pistorius a Kotu

Zakaran dan wasan tseren nakassasun nan, Oscar Pistorius ya harbi budurwarsa Reeva Steenkamp sau uku a lokacin da take bandaki, a cewar masu gabatar da kara.
Ana kara samun bayanai game da kisan Reeva ne, a zaman kotun da ake ayi rnar Talata a Afirka ta Kudu, inda za a duba yiwuwar daba bellin Oscar.

Pistorius ya fashe da kuka a yayin da ya ji tuhumar da ake masa na kisan budurwarsa da gangan, amma lauyansa ya shaida wa kotu cewa bai aikata kisan kai ba.
Zaman kotun da ake yi Pretoria na zuwa ne a rana daya da jana'izar Reeva a Port Elizabeth.
Mai shigar da kara Gerrie Nel ya bayyana wa kotun cewa, a daren da lamarin ya auku, Oscar wanda bashi da kafafuwa ya sanya kafafuwan karfensa kuma ya yi tafiya na mita bakwai, sannan ya harbi kyauren bandakinsa.
Ya yi harbi sau hudu, inda ya samu Steenkamp sau uku, kuma daga bisani ya balla kyauren bandakin ya dauke ta ya kaita kasa, Inji Mr. Nel.
Sai dai lauya mai kare wanda ake kara, Barry Roux ya shaida wa kotu cewa, zakaran wasan bashi da masaniyar cewa tana bandakin, kafin yayi harbin.
Saboda haka masu gabatar da karar basu da wata shedar cewa da gangan ya kashe ta, don haka bai aikata kisan kai ba.

No comments:

Post a Comment