Wednesday, 20 February 2013

AC Milan ta casa Barca

ac milan barcelona

Kungiyar AC Milan ta Italiya ta lallasa Barcelona ta Spaniya da ci 2-0 a wasan cin Kofin Zakarun Turai.
Wannan karawar farko ce ta kungiyoyi 16 wadda bayan karawa ta biyu za a fitar da guda 8 da za su yi wasan gab da na kusa da karshe.
Boateng ne ya fara jefa kwallo a ragar Barcelona a minti na 57, kafin minti na 81 kuma Sule Muntari ya kara ta biyun.
A daya wasan na cin Kofin na Zakarun Turai, Galatasaray ta Turkiyya ta yi 1-1 da Schalke 04 ta Jamus.
Yilmaz ne ya ci wa Galatasaray kwallonta a na minti 12 da fara wasa.
Ana gab da tafiya hutun rabin lokaci a minti na 45 Jones ya rama wa bakin .
A ranar 12 ga watan Maris ne za ayi karo na biyu na wasannin.

No comments:

Post a Comment