Wadansu attajiran da ke da hannun jari a harkar
intanet ciki har da mutumin da ya samar da shafin facebook, Mark
Zukerberg, sun sanya gasa mafi girma a fannin kimiyya.
An sanya gasar ce saboda nuna irin gudunmawar da
masu nazarin kimayya suka bayar a duniya da zummar karfafawa matasa
gwiwa don su karanta fannin.Za a ware mutane biyar da suka fi yin fice a fannin kimiya a duk shekara, sannan a ba kowane kyautar da ta kai dala miliyan uku.
A cewar Mark Zukerberg, yin hakan zai sanya duniya ta sani cewa ba wai kawai shahararrun 'yan wasan kwallo da taurarin fina-finai ne kadai ke taka rawa a duniya ba, har ma da masu nazarin kimiyya.
Abin alfahari
Kudin da za a bai wa wanda ya lashe gasar ya ninka kudin da ake bai wa mutumin da ya lashe kyautar Nobel.Kowa na iya shiga gasar sai dai manufar ita ce a karrama masana kimiyyar da ke tashe yanzu, ba wadanda suka gaba ce su ba.
Ana kallon hadin gwiwar da wadannan 'yan kasuwa suka yi a matsayin wani abin alfahari idan aka yi la'akari da yadda suke zafafa gasa a tsakanisu kan yadda kowanne zai fi dan uwansa karbuwa a fannin intanet.
Mark Zukerberg ya ce 'yan jarida ne kawai ke kambama rashin jituwar da ke tsakanin google da facebook da kuma apple .
A bana dai, an bai wa wadansu masu nazarin kimiyya su goma sha daya kyautar dala miliyan uku-uku, saboda binciken da suka yi a kan dalilan da ke kawo cutar daji, da ciwon sukari da maganin cututtukan da kuma inganta rayuwa dan adam.
No comments:
Post a Comment