
Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi, ya yi kira da a fara gudanar da zaben majalisun dokoki daga karshen watan Aprilu mai zuwa.
Wata sanarwa da shugaban kasar ya fitar ta ce
za a fara zaben ne daga ranar 27 ga watan Aprilu, a kammala a karshen
watan Yuni.Sanarwar ta ce za a gudanar da zabukan ne a matakai gudu hudu, kuma daga yanki zuwa yanki.
Za a gudanar da zaben ne daki-daki a yankuna daban-daban ne saboda karancin masu sanya idanu a kan zabe.
No comments:
Post a Comment