Wednesday, 20 February 2013

'Yan bindiga a Najeriya sun sace 'yan Kasashen waje a Bayelsa

Mohammed Abubakar Babban Spetan 'yan sandan Najeriya

Wasu 'yan bindiga a Najeriya sun sake sace ma'aikata 'yan kasashen waje shida.
'Yan sanda sun ce maharan sun shiga cikin wani jirgin ruwan daukar mai ne a gabar ruwan Bayelsa ranar Lahadi.
Mutanen da aka kama sun fito ne daga kasashen Ukraine, India da kuma Rasha.
Hukumar SSS a Najeriya ta yi kame
A wani bangaren kuma Hukumar Leken Asiri ta kasar SSS, ta cafke wani mutum mai kimanin shekarau 50 mai suna Abdullahi Mustapha Berende dan asalin jihar Kwara, da take zargin da hannu wajen aikata laifin leken asiri da ta'addanci a kasa, tare da hadin gwiwar wasu 'yan kasar Iran.
Hukumar ta SSS din ta kuma ce a bisa bincike, da sa idon da ta dade tana yi, wanda ake zargin ya sha yin tafiye-tafiye zuwa kasar Iran, domin tattaunawa da wasu Iraniyawan da suka dade suna jagorancin wata kungiyar 'yan ta'adda ta kasa da kasa, da yanzu haka ke yunkurin cimma wasu manufofi a Najeriyar

No comments:

Post a Comment