wasanni

 ac milan barcelona


Kocin AC Milan ya ce ba kamar yadda kowa ya ke dauka ba ba za ayi musu kaca-kaca ba idan suka hadu da Barcelona a karawarsu ta cin Kofin Zakarun Turai.
Massimiliano Allegri ya ce ''mun san cewa za mu hadu ne da kungiyar da tafi kowace kungiya a duniya amma ba zan yarda cewa za a lallasa mu ba.''

Milan wadda ta fara kakar wasan bana tana tangal-tangal ta farfado har ta kai matsayi na 4 a gasar Serie A ta lig din Italiyan.
Barcelona kuwa a yanzu ita ce ta daya da maki 12 a lig din Spaniya da take kan hanyar karbe kofin daga abiyar hamayyarta Real Madrid.
Mataimakin kocin Barcelona Jordi Roura wanda ke jagorantar klub din a wannan karawa yayin da ake yiwa kocin Tito Vilanova maganin ciwon dajin da yake fama da shi ya ce ba kungiyarsu ce za a ce zata yi nasara ba.
Yace idan manyan kungiyoyi suka hadu a wannan mataki ba za a ce wata ta fi wata ba .
Roura ya ce muna mutunta Milan sosai wadda ta fi kowa daukar kofin na zakarun Turai.
Ita dai AC Milan sau 7 tana daukar Kofin na Zakarun Turai, yayin da Barcelona ta dauka sau 4.
Barcelona ba ta taba rashin nasara a haduwarta da AC Milan din ba.
A karawarsu a bara a gasar ta Kofin sun yi canjaras sau biyu a wasan rukuni, a wasan gab da na kusa da karshe kuwa Barcan ta yi galaba sau biyu. 

No comments:

Post a Comment