Gwamnatocin Faransa da Nijeriya sun musanta wasu
rahotanni da ke cewar an gano Faransawar nan bakwai da aka yi awon gaba
dasu a arewacin Kamaru.
Tun farko dai, Ministan kula da 'yan mazan jiya
na kasar Faransa ya bayayna a gaban majalissar dokokin Faransa cewa an
gano Faransawan a wani gari a arewacin Nigeria, amma daga bisani ya
janye maganarsa yana mai cewar babu wani tabbasci a kan labarin.An dai yi ta samu rahotanni masu karo da juna a kan al'amarin, inda wata majiya ta sojojin Kamaru ita ma ta ce an gano Faransawan.
Rahotanni na baya baya na cewa an gano inda ake rike da Faransawar, kuma jami'an tsaro sun kewaye wurin, sai dai babu wata majiyar tsaro da ta tabbatar da gaskiyar hakan ya zuwa yanzu.
No comments:
Post a Comment