Asalin Hausawa abu ne da aka sha kuma ake kan tambaya a kullum, sai dai abin takaici har
yanzu ba a sami wata cikakkiyar amsa mai gamsarwa ba. Kafin mu yi nisa ya kamata mu san
ko su wane ne Hausawa. Hausawa dai su ne mutane wadanda harshensu shi ne Hausa
sannan dukkan al’adunsu na Hausa ne. Haka kuma addinin musulunci ya yi cikakken tasiri a
kansu.
Mutane dabam-daban sun yi bincike sosai a kan ilmin harsuna da abubuwan da aka kattaba da
kuma zantukan baka. Ta hanyar irin wannan bincike ne aka gane cewa wadansu harsuna suna
da kama da juna ainun, wanda ya haifar da kara zurfafa nazarce-nazarce. Sakamakon haka ne
kuwa aka karkasa harsunan Afrika ta yadda kowane kaso ya kunshi harsuna wadanda bisa
dukan alamu tushensu guda. Ma’ana a asali su wadannan harsuna harshe ne guda daya
wanda wasu dalilai irin su bambancin wurin zama, sanadin kaurace-kaurace da yake-yake da
dai wadansu dalilai suka sanya ya karkasu ya kasance harsuna iri-iri a halin yanzu.
Akwai dangunan harsuna da dama a cikin Afrika. Misali akwai dangin Bantu a can wajen
tsakiyar Afrika wadanda tushensu duka daga wani tsohon harshe ne wai shi Bantu; akwai kuma
dangin Kwa wanda ya kunshi Yarabanci da Ibo da Nupanci da dai sauransu. Ita kuwa Hausa
tana cikin harsunan iyalin Cadi. Ko da yake shi wannan harshe babu shi a yanzu, wannan suna
na Cadi suna ne kawai da masana ilmin harsuna suka kirkiro. Dalili kuwa shi ne yawancin iyalin
wannan harshe ana samunsu a farfajiyar tafkin Cadi. To saboda rashin sanin ainihin sunansa sai aka kira shi da sunan Cadi. Harsunan iyalan Cadi suna da yawa. Akwai Angas da Bacama da Bade da Bolanci da Bura da Hausa da Kanakuru da Karekare da Mandara da Margi da Miya da Ngizim da Tera da dai sauransu. A sakamakon kamanni da wadannan harsuna suke yi da juna ya sanya aka danganta su ga tushe guda. A bisa wannan dan bayani muna iya cewa Hausawa da harshensu sun fito ne daga cibiya daya da sauran harsunan iyalin Cadi. Wannan kuwa zai ba mu damar cewa mutanen da suka zama Hausawa sun fito ne daga Gabas ko arewa maso gabas da wurin da suke a yanzu Daga nan sai mu duba abubuwan da aka kattaba. A nan an samu mutane dabam-daban sun yi rubuce-rubuce a kan asalin Hausawa da harshensu. A wani littafi da ya wallafa a kan Daular Usmaniyya, Johnston ya bayyana cewa a tsakanin shekarar 1050 zuwa 1100 ta Miladiyya wadansu, Berbers, (Buzaye) sun ratso sahara suka zauna cikin Tukururu kuma suka yi auratayya da su. Wai a sanadin wannan cudanya ne aka sami Hausa da harshen Hausa. Shi ma wani marubucin dangane da tarihin Hausawa da harshensu, M.G. Smith, yana da ra’ayi kusan iri daya da na Johnston. Wato ya amince da cewa akwai kaura da ta auku daga gabas zuwa kasar Tukururu, wanda ya yi sanadin samuwar Hausawa da harshensu. Ya kare da cewa wannan kaura ta auku ne wajajen shekarar 1350 ta Miladiyya. Shi kuwa Abdullahi Smith nuna rashin amincewarsa ya yi da wannan bayani da aka yi dangane da asalin Hausawa da harshensu. Musamman ma cewa wai nan da shekara dubu da suka wuce babu Hausawa. Shi yana ganin cewa kasa rarrabewa tsakanin asalin Hausawa da harshensu da kuma asalin daular mulkin da suka kafa shi ne dalilin rashin fahimtar. Haka kuma bai amince ba da cewa Hausawa sun samu a sakamakon auratayya tsakanin Berbers (Buzaye?) da kuma Tukururu da suka taras a wurin. Hasali ma ra’ayinsa ya fi karkata ga cewa Hausa tana da alaka da harsunan iyalin Cadi, har hakan ma kuwa yana ganin cewa sun raba hanya shekaru dubbai da suka wuce.Ya kuma kara da cewa mai yiwuwa da can akwai dangantaka tsakanin harshen Berber da na Cadi, wato tun kafin Sahara ta zamo hamada. Babu shakka ba abu ne mai karbuwa ba a ce nan da shekaru 950 da suka wuce babu Hausawa da harshensu, musamman idan aka dubi tarihin garuruwan Hausa da jerin sarakunan da suka mulke su. Misali an ce tun karshen karni na 9 na Miladiyya wadansu maharba suka zo suka zauna a duwatsun da ke kewaye da sararin da ake kira Kano yanzu. Idan haka
zamu cigaba gobe Inshaallahu
No comments:
Post a Comment