Wani bam ya tashi da yammacin jiya lokacin da wadansu
maharan suka tunkari motocin sunturi na jami'an tsaro na Rudundunar
Hadin Gwiwa ta JTF a kasuwar Gambaru, daura da babbar hanyar zuwa
Gamboru-Ngala a Jihar Borno da ke arewacin Najeriya.
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta JTF ta
tabbatar da faruwar al'amarin, tana mai cewa sanadiyar fashewar bam din
wuta ta watsu ta kona gidaje da shagunan da ke kewaye da wajen.A sanarwar mai dauke da sa hannun kakakinta, Laftanar Kanar Sagir Musa, rundunar ta ce mutane biyu—wadanda ake zargin maharan ne—da wani soja daya sun rasa rayukansu.
Ta kuma ce bam din ya yi kaca-kaca da wata motar rundunar ta JTF, ko da yake babu wani farar hula da abin ya shafa.
No comments:
Post a Comment