
Iyalan ma'aikatan rigakafin shan inna ko polio da aka
kashe a jihar Kano a makon jiya, sun samu tallafin naira miliyan daya
kowannensu.
Gwamnatin jihar ce ta basu naira dubu dari
biyar, yayin da shahararren mai kudin nan na Najeriya, kuma dan asalin
jihar Aliko Dangote, kuma ya basu tallafin naira dubu 500. Kimanin mata tara ne suka mutu a lokacin da wasu 'yan bidiga suka bude musu wuta a ranar Juma'ar data gabata.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran ministan lafiya na kasar zai kai ziyara jihar Kano game da harin.
No comments:
Post a Comment