Sakamakon farko-farko na zaben shugaban kasar da aka
gudanar ranar Lahadi a Ecuador ya nuna cewa Shugaba Rafael Correa ya yi
nasarar samun damar ci gaba da rike mukaminsa.
Adadin kuri’un da dama aka yi hasashen shugaban
kasar mai ra’ayin gurguzu zai samu ya kai yadda ba sai an je zagaye na
biyu ba kuma tuni ma dai abokan hamayyarsa suka amince da shan kaye.
No comments:
Post a Comment