
Jami’an tsaro a Najeriya sun ce suna farautar wadanda suka sace ma’aikatan wani kamfanin gine-gine ’yan kasashen waje su bakwai.
An sace ma’aikatan ne masu aiki da kamfanin Setraco mallakar ’yan kasar Lebanon a garin Jama’are na Jihar Bauchi dake arewa maso gabashin kasar.
An bayyana cewa wadanda aka sacen a abin da ake ganin satar mutane mafi girma a arewacin Najeriya a dan tsakanin nan, sun hada da dan kasar Italiya, da dan kasar Philippines, da dan kasar Burtaniya, da dan kasar Girka da kuma ’yan kasar Labanon.
Wakilin BBC a Jihar ta Bauchi ya ce maharani sun datse hanyar zuwa gidan da mutane suke, sannan suka kai hari a kan ofishin ’yansanda na yankin da gidan yari—ko da yake ba su kubutar da fursunoni ba.
Maharan, a cewar wakilin na BBC, Is'haq Khalid, sun shiga cikin gidan kwanan ma’ikatan dake wani wuri da ake kira Life Camp ne ta hanyar fasa ginin da bama-bamai daga ta baya, suka kashe mai gadi ɗaya, sannan suka sace mutanen.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar ta Bauchi, Alhaji Abubakar Ladan, ya tabbatar da sace ’yan ƙasashen wajen bakwai.
Babu asarar rai ko jikkata
Kwaminishinan ya kuma tabbatar da kai hari a kan ofishin ’yan sandan dake kusa da wajen amma ya ce babu asarar rai ko jikkkata sai dai an ƙona motocin yan sanda guda biyu.Shi dai kamfanin na Setraco, kamfanin gine-gine ne mai hedikwata a Abuja, yana kuma ayyukan kwangiloli musamman na gina hanyoyin mota a Najeriya, kuma ma’aikatansa sun hada da ’yan Nijeriya da ’yan kasashen waje.
Har yanzu ’yan sanda ba su gano ko su waye suka kai harin ba, kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace mutanen.
A Najeriya dai an sha samun sace-sacen mutane ’yan ƙasashen waje, inda a wadansu lokutan akan yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa.
No comments:
Post a Comment