Wednesday, 27 February 2013

Tana dabo tsakanin Keshi da NFF

 Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi

Mai horar da 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya, Stephen Keshi ya ce rashin jituwar dake tsakaninsa da hukumar kwallon kafa ta kasar, tana kasa tana dabo.
Keshi da ya yi tayin yin murabus, 'yan sa'oi kadan bayan kungiyar Super Eagles ta dauki kofin gasar zakarun kwallon kafa na Afirka, wanda rabon kasar da daukar kofin tun shekarar 1994.

Sai dai ya sauya shawara bayan wani taron gaggawa da ministan wasannin kasar, Bolaji Abdullahi a Johannesburg.
A wani shirin talabijin na turanci, Superspost a ranar Litinin da daddare, Keshi ya ce 'yar masalahar da aka samu tsakaninsu, wacce ta dan so ta kawo tsaiko ga shagulgulan murnar daukar kofin, na wani dan lokaci ne.
"A halin yanzu ina da kyakkyawar dangantaka da shugabana (Aminu Maigari) baya ga mutum daya ko biyu a hukumar" Keshi ya fadi hakan a shirin da ake watsa wa kai tsaye.
Ya kuma kara da cewa "Idan na gaji da zaman da na ke yi, kuma idan har bana jin dadin abin da nake yi, kawai tafiya ta zanyi."
"Sama da kasa ba za ta hade min ba, idan na daina horar da 'yan wasan Najeriya."
"Amma dole a bani girma na, kuma a barni in yi aiki na ba tare da tsoma baki ba." Inji Keshi.
Keshi shi ne bakar fata na biyu da ya taba daukar kofin gasar, a lokacin yana dan wasa da kuma a matsayin mai horar da 'yan wasa a nahiyar Afrika.
Kuma shi ne koci bakar fata na farko, da ya taba daukar kofin tun bayan shekarar 1992.

No comments:

Post a Comment