
Rahotanni daga jihar Filaton Najeriya na cewa 'yan
bindiga da a ba san ko su wanene ba sun kashe mutane tara a harin da
suka kai a yankin Vom a ranar Alhamis da daddare.
Sai dai kwamishinan 'yan sandan jihar, Mista Chris Olakpe, ya shaidawa BBC cewa gawarwakin mutane hudu suka gano.Jihar Filato dai ta dade tana fama da rikice-rikicen da suke da dangantaka da kabilanci da addini da kuma siyasa.
Karar harbe-harbe a Maiduguri
Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, na cewa an shafe daren ranar Alhamis ana jin karar harbe-harben bindigogi a sassa daban-daban na birnin.Sai dai har yanzu ba a san ko wannan lamari ya yi sanadiyar mutuwa ko jikkata mutane ba.
Ko a ranar Laraba ma , akalla mutane takwas ne suka mutu sanadiyar fashewar wani abu da ake zaton bam ne a unguwar Kwastan da ke birnin.
Haka kuma shaidu sun ce bakin hayaki ya turnike sararin samaniya, kuma shaguna da dama sun kone.
No comments:
Post a Comment