Alhaji Bamanga tukur Shugaban jam'iyyar PDP, Na kasa da sabon shugaban kungiyar gwamnonin PDP zalla, Mr Godswill Akpabio sun furta kalamun da suka gasgata zargin da Janar Muhammadu Buhari ya yi a ranar Litinina Abuja yayin da yake ganawa dazababbun wakilan jam'iyyarsa ta CPC,
inda ya ce jam'iyyar PDP a halin yanzu ta kideme, ta kuma dukufa don ganin ta ci zabe mai zuwa ko ta halin kaka. Alhaji Bamanga ya ce yanzu Shugaba Goodluck Jonathan zai iya shara barci har da
minshari tun da an cire masa kaya, wato an raba shi da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Mr Rotimi Amaechi don ya ki amincewa Jonathan ya yi wasan kura da gwamnoni don daurewa karya gindi wajen tsayar da shi takara a la dole.
Ya furta haka ne sa'ilin da yake marhabin da shugaban sabuwar kungiyar gwamnonin PDP zalla, Mr
Godswil Akpabio sa'ilin da ya kai masa ziyarar ban girma a ofishnsa. Shi ma Mr
Akpbio ya ce jam 'iyyar PDP ta yi shirin tankade duk wadanda ke adawa da sake takarar Shugaba Jonathan, kuma komai girman mukamansu za a yi watsi da su don kar su kawo cikas. E, lalle! Janar Buhari ya yi gaskiya! Jam'iyyar PDP ta kauce daga bisa turbar dimokuradiyya, ta hau ta kama-karya don aiwatar da harkokinta na cikin gida. Abin cewa shi ne a yi dai mu gani, gaba mu bayar da labri wasa ya yi kyau, ko ya kazance! Shure-shure dai bai hana mutuwa.
No comments:
Post a Comment