Thursday, 14 February 2013

An harbe wani matashi a zanga zangar Bahrain

 Zanga Zanga a Bahrain

An harbe wani yaro har lahira a kasar Bahrain, a lokacin wata zanga-zanga domin cika shekaru biyu da juyin-juya halin da baiyi nasara. Wasu mutenen da dama sun samu raunuka lokacin da masu zanga-zangar adawa da gwamnati suka kafa shingaye akan hanya sannan suka yi arangama da jami'an tsaro. Gwamnatin Bahrain ta tabbatar da mutuwar wani yaro dan shekaru sha shida amma tace ba a san dalilan mutuwar ta sa ba. Wani mai fafutuka na 'yan adawa Radi Al-Musawi, ya shaida wa sashin Larabci kan yadda lamarin ya faru

No comments:

Post a Comment