
An sauya jami'in dan sandan da ke jagorantar binciken
kisan kan da ake zargin Oscar Pistorius da shi, bayan da ta bayyana
cewar shi kansa ya na fuskantar tuhume-tuhume bakwai na kokarin aikata
kisan kai, shekaru biyun da suka wuce.
Kwamishinar 'yan sanda ta kasa a Afrika ta Kudu,
Mangwashi Victoria Phiyega ce ta bayar da sanarwar inda tace 'Na yanke
shawarar wannan muhimmin batu , wannan muhimmin bincike a karkashin
shugabanci da jagorancin Kwamishin gunduma kan ayyukan bincike, Lt Janar
Moonoo'.Shi dai dan tseren, Oscar Pistorius, ana zarginsa ne da kashe budurwarsa, Reeva Steenkamp.
A gobe Juma'a, ake sa ran za a yanke hukunci game da shari'ar neman belin da aka shigar kan Mr Pistorius.
No comments:
Post a Comment