A ranar Talatar da ta gabata ne aka gurfanar da tsohon Darakata Janar
din Hukumar Tace Fiian-finai ta Jihar Kano, Malam Rabo Abdulkarim da
‘yan jarida da ke aiki da gidan rediyon Wazobiya wadanda suka hada da
Yakubu Musa Fagge da Mubarak Sani Muhammad
, a gaban wata kotun majistare mai lamba 17 da ke unguwar Gyadi-gyadi
cikin Jihar Kano bisa zarginsu da laifin hadin baki bisa tunzura jam’a
su kyamaci allurar rigakafin shan inna tare da cin zarafin Hakimin
Tarauni dan goribar Kano a cikin shirin gidan rediyon wazobiya na
‘Sandar Girma.’
Tunda farko mai gabatar da kara Sajan Sadik Na’abba a
cikin takardar karar da ya karanta a gaban kotun ya bayyana cewa,. “Kai
Malam Rabo Abdulkarim wanda ke zaune a gida mai lamba 155 a kan titin
Maiduguri a karamar Hukumar Tarauni ka bijire wa ma’aikatan allurar
rigakafin shan inna inda ka nuna ba za su yi wa ‘yayanka ba. Hakan ya
jawo Hakimin Taruni da sauran shugabnnin da ke kula da aikin allurar
suka je gidanka don sanin dalilinka na kyamar allurar. Amma sai aka samu
ka hada baki da wadansu ‘yan jarida da ke aiki a gidan rediyon Wazobiya
inda suka gabatar da wani shiri na ‘ Sandar Girma’ don tunzura jama’a
su kyamaci allurar Foliyo din tare da cin mutuncin Hakimin Tarauni. Har
ila yau kuma hakan shi ya yi sanadiyar da aka kai wani hari har aka
kashe wasu ma’aikatan foliyo a kanan hukumomin Tarauni da kuma Nassarawa
wanda hakan laifi ne da ya saba wa sashe na 97 da 85 da 399 da 392 da
393 na kundin laifuka na Finalkod (pinal code).
Sai dai dukkanin wadanda ake zargin sun musanta laifin da ake zargin su da shi.
Mai
shari’a Bello Ibrahim ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 14 ga wannan
watan don ci gaba da sauraran shari’ar, tare da bayar da umarnin ci
gaba da tsare wadanda ake zargi har zuwa ranar da za a ci gaba da
saurarn shari’ar.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano dai ta kama ‘yan
jarida wadanda ke aiki da gidan rediyon Wazobiya FM da kuma tsohon
Darakta Janar na Hukumar tace Fina-finai ta Jihar Kano, Malam Rabo
Abdulkarim ne inda take bincikensu game da wani shiri da gidan rediyon
ya watsa a makon da ya gabata a game da cutar foliyo.
‘Yan jaridar da
‘yan sandan suka kame sun hada da Shugaban sashin shirye-shirye na
gidan rediyon Wazobiya Muhammad Sulaimanu Gama da kuma maishiryin wani
shiri mai suna ‘’Sandar girma’’ Yakubu Musa Fagge da kuma mai dauko
rahoto, Mubarak Muhammad Sani.
Shugaban gidan rediyon na Wazobiya
Malam Sanusi Bello Kankarofi ya bayyana wa Aminiya cewa, a ranar Lahadin
da ta gabata ne rundunar ‘yan sandan ta gayyaci ma’aikatansu guda uku
don bincike. “Tun daga wancan rana kuma aka tsare ma’aikatan namu ba
tare da wani dalili ba. Mun nemi su sanar da mu wane shiri ne muka sanya
a rediyo wanda har ya jawo aka aiwatar da hari a kan ‘yan sandan da ke
yi wa ma’aikatan alluar rigakafin cutar shan inna rakiya, amam sun kasa
ba mu amsa. Mu muna ganin ana so a yi amfani da wannan dama ne a
wulakanta ‘yan jarida saboda wani dalili na siyasa.” Inji shi.
Sai
dai a hirar da ya yi da manema labarai, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar
Kano Alhaji Ibrahim K. Idris ya musanta wannan zargi, inda ya ce, “Babu
shakka mun kama wadannan mutane, sai dai ba mu kama su a matsayinsu na
‘yan jarida ba, sai don gudanar da wani bincike da muke yi. Da zarar mun
kammala bincikenmu za mu sanar da jama’a halin da ake ciki.” Inji shi.
Aminiya
ta samu damar tattaunawa da Malam Rabo Abdulkarim a lokacin da yake
tsare, inda ya bayyana wannan kame a matsayin cin zarafin bil’Adama,
“Tun da dai mun san a kan gaskiya muke to muna yi wa Allah godiya.
Babban fatanmu shi ne game da wannan ma’amala ta allurar rigakafin shan
inna a daina tursasa talakawa a kai, ba wai a kan wannan kawai ba,
dukkanin wadansu abubuwa da aka kawo komai kyawunsu bai kamata a
turasasa jama’a a kai ba. Abin da ya kamata a yi shi ne a yi kokarin
ilimantar da jam’ar har su gane alfanun da ke cikin lamarin. Yadda mutne
za su rika yin mua’amala kowace iri ce bisa ra’aiyin kansu da kuma bisa
ilimantar da su da aka yi.”
Shi ma a nasa bangaren, mai gabatar da
shirin na ‘Sandar Girma’ Yakubu Musa Fagge ya bayyana cewa babu wani
abu na hadin baki tsakanin gidan rediyonsu da Malam Rabo wajen aikewa da
ma’aikacinsu, haka kuma ba shirinsa na Sanda ne ya jawo aka kai hari
kan ma’aikatan foliyo ba. “Gaba daya dai laifin da ake tuhumarmu da shi,
shi ne mun hada baki da Malam Rabo wajen aika wakilinmu don ya dauki
rahoton takaddamar da za ta faru tsakaninsa da masu allurar shan inna.
Hakan ya sa na ba wa ‘yan sandan hujjoji guda uku wadanda suka karyata
hakan, sai dai sun ce har yanzu suna nan suna gudanar da bincike. Haka
kuma shirinmu na Sanda ba shi ne ya jawo aka kai hari a kan ma’aikatan
foliyo ba.” Inji Yakubu.
Aminiya ta samu zantawa da Shugaban sashin
shirye-shirye na gidan Rediyon Wazobiya Muhamamd Sulaiman Gama jim kadan
bayan an bayar da belinsa, ya bayyana wa Aminiya cewa duk da cewa ba a
gaya musu laifin nasu kai tsaye ba, amma an sanar da su cewa shirinsu na
Sanda shi ne ya tunzura jama’a kyamatar allurar rigakafi, haka kuma
shirin ne ya jawo ‘yan bindiga suka kai hari a kan ma’aikatan foliyo.
“Rigimar ta fara ne bayan an doki ma’aikacinmu a lokacin da ya dauki
rahoto a kan rigimar rigakafin allurar tsakanin Malam Rabo da tawagar
masu tabbatar da cewa an yi allurar har aka kwace masa kayan aikinsa,
hakan ya sanya mai gabatar da shirin Sanda ya tabo waccan magana a cikin
shirinsa wacce kuma ba ta yi musu dadi ba. Haka kuma sai ga shi
washegri an kai hari kan masu allurar rigakafin har aka kashe mutum tara
a cikinsu. Wannan ne ya sa aka ce ana tuhumar ma’aikatanmu.” Inji shi.
Binciken
Aminiya ya gano cewa ‘yan sanda suna kokarin hada alaka tsakanin shirin
da gidan rediyon Wazobiya ya gabatar da kuma harin da aka kai washegari
kan ma’aikatan foliyo a jihar, inda suke zargin shirin na sanda da hura
wuta tare da tunzura jama’a kyamar allurar polio.
Idan za a iya
tunawa a ranar Talata biyar ga watan Fabreru dan jarida da ke aiki da
gidan rediyon Wazobiya ya sha da kyar sakamakon dukan da wadansu matasa
suka yi masa a daidia lokacin da yake gudanar da aikinsa.
Kamar yadda
dan jaridar da ya sha dukan mai suna Mubarak Muhammad Sani ya bayyana
wa Aminiya, ya ce a daidai lokacin da yake hira da tsohon Shugaban
Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Malam Rabo Abdulkarim a gidansa a
kan wani lamari daban, sai ga tawagar da ke lura da allurar rigakafin
sun shigo gidan wadanda suke son ganin Malam Rabo a kan wata magana ta
daban. “Lokacin da muke tattunawa da Malam Rabo sai tawagar masu allurar
rigakafin, da ta kunshi Shugaban Riko na karamar Hukumar Tarauni da
Hakimin Tarauni da kuma wadansu ‘yan bangar siyasa,da wanda na ke zaton
‘yan jam’iyyar PDP ne, domin dukkaninsu suna sanye da jajayen huluna,
sai suka shigo gidan inda suka nemi mu dakatar da abin da muke yi har
sai sun gama abin da ya kawo su gidan. A lokacin da na fuskanci
tirka-tirka da mujadala ta kaure a tsakaninsu sai na fara daukar
labarin. Yayin da suka fuskanci abin da nake yi sai Hakimi ya ba wa
matasan nan umarni da su fitar da ni waje tare da duka na.”
dan
jaridar ya kara da cewa, “Na yi kokari wajen fahimtar da su abin da ya
faru amma suka ki saurara ta, inda suka yi kwallo da ni zuwa waje, suka
yi min duka, ta hanyar hada hannayensu bibbyu suka rika dukana a fuskata
da gefen kunnuwana. Saboda tsananin duka wallahi kasa gane abin da yake
faruwa na yi. Sai na rika jin wani dum a kaina.”
Malam Mubarak wanda
yake kwance a gida yake jinyar raunikan da ya samu a lokacin wanann
waki’a, ya bayyana cewa, tawagar ta kwace wayarsa da rediyon daukar
maganarsa tafi da su, sai da shugabanninsa suka sanya baki sannan aka
dawo masa da kayayyakinsa.
A lokacin da Aminiya ta tuntubi mai
taimaka wa Gwamnan Kano a kan harkokin watsa labarai, Ja’afar Ja’afar ya
musanta faruwar wannan lamari, inda ya ce babu wani mutum mai halkali
da zai sa a doki wani, ballanatan kuma bababn mutum kamar Hakimi.
“Wanann magana babu gaskiya a cikinta. Ta yaya ma babbn mutum kamar
Hakimi zai sa a doki dan jarida. Ban da ma haka yaya za a yi a tabbatar
da cewa mutanen da suka yi dukan ‘yan PDP ne don kawai sun sanya jar
hula? Kowa ma zai iya sanya jar hula ya badda kama a matsayin dan
jam’iyyar PDP.” inji Ja’afar.
A washegarin ranar Laraba ne a cikin
shirin Sandar Girma gidan rediyon Wazobiya ya bayar da rahoto game da
dukan kawo wuka da aka yi wa wakilinsu a lokacin da yake gudanar da
aikinsa na daukar rahoto a kan tirka-tirkar da ke faruwa game da allurar
rigakafin cutar shan inna. An ce dai wanann shiri ne ya ja musu
jangwam inda ake zarginsu da laifin tunzura jama’a bisa kyamar allurar
rigakafin.