Monday, 4 March 2013

Yara 800 sun kamu da kyanda a jihar Kano

 Yaro mai fama da cutar gyanda

An samu barkewar cutar kyanda a jihar kano dake arewacin Najeriya, abin da ya sa yara fiye da 800 ke yin jinya a asibitoci daban-daban na jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran yusuf ne ya tabbatar wa yan neman labarai hakan.
Amma dai wasu majiyoyin sun ce yara fiye da dubu daya ne suka harbu da cutar.
Dr. Abubakar ya ce barkewar cutar na da nasaba da shigowar zafi, inda ya nemi iyaye su yi ta kai yaransu rigakafi.
Sai dai wasu rahotannin na cewa an samu karancin allurar rigakafin cutar, abin da ya taimaka wajen barkewarta.
Cutar ta barke ne a wasu kananan hukumomi biyar da suka hada da Tarauni da Gwale da Madobbi da Karaye da kuma Kabo.

No comments:

Post a Comment