
Sabon Zababban Shugaban Kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya
dau alkawarin aiki tare da wanda ya kayar, kuma abokin hamayyarsa Raila
Odinga, da kuma yiwa dukkanin 'yan Kasar Kenya aiki a kalamansa ba kuma
tare da tsoro ko nuna alfarma ba
An bayyana Mr Kenyatta wanda ya lashe zaben na
ranar litinin da 'yar karamar , inda ya samu kashi hamsin da digo bakwai
cikin dari na kuri'un da aka kadaAmma Mr Odingan yace zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.
Ya kuma yi gargadin cewar duk wani tashin hankali ka iya dagula kasar
Mr Kenyatta dai na fuskantar shari'ah a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake Hague, bayan da aka zarge shi da hannu a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekarar 2007
No comments:
Post a Comment