Monday, 11 March 2013

Burkutu ta kashe mutane da dama a Libya

Libya

Mutane sama da hamsin ne ake cewa sun mutu daga cikin daruruwa da aka kwantar a asibitoci a duk fadin Turabulus, babban birnin kasar Libya, sakamakon shan gurbatacciyar giyar gargajiya wato burkutu.
Ma'aikatar lafiya ta Libyar ta yi shelar cewa an shiga wani yanayi na ta-baci, a asibitocin kasar.
Tun daga ranar Asabar aka fara samun mace macen, kuma adadin ya ci gaba da karuwa.

No comments:

Post a Comment