
Ma'aikatan kiwon lafiya a Guinea sun ce, an kashe
mutum guda, wasu da dama kuma sun jikkata yayin da jami'an tsaro suka
budewa wasu mutane wuta a yankin Koloma na Conakry, babban birnin kasar.
Wannan lamari dai ya biyo bayan kwanaki ne da
aka kwashe ana tashin hankali a birnin tsakanin masu goyon bayan
bangaren adawa da kuma jami'an tsaro, da kuma wadanda basa ga maciji da
juna daga kabilu daban-daban.Su dai 'yan adawar kasar suna nuna rashin nuna rashin amincewa ne da zaben da ake shirin yi cikin watan Mayu, suna zargin cewa, gwamnati ta shirya murde zaben.
No comments:
Post a Comment