Friday, 1 March 2013

Goodluck Jonathan zai iya tsayawa takara a 2015'

Goodluck Jonathan

Wata kotun tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta ce shugaban kasar Goodluck Jonathan zai iya tsayawa takara a zaben shekara ta 2015.
Kotun ta ce sai a shekara ta 2015 ne zai kammala wa'adinsa na farko.

Goodluck Jonathan ya fara wa'adinsa ne bayan zaben da aka yi masa a shekara ta 2011.
Ta kara da cewa mulkin da ya hau a shekara ta 2010 bayan rasuwar marigayi Shugaba Umaru 'Yar'adua, ya zama wajibi ne domin cike gibin da aka samu kamar yadda tsarin mulki ya tanada.
Wani dan jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ne ya shigar da karar yana neman kotu ta hana shugaban tsayawa takara bisa hasashen cewa ya yi wa'adi biyu a kan karagar mulki.
Wakiliyar BBC da ta halarci zaman kotun Raliya Zubairu, ta ce lauyoyin da suka wakilci jam'iyyar PDP sun nuna farin cikinsu ga wannan hukunci, sai dai wanda ya shigar da karar ya ce zai daukaka kara zuwa kotu ta gaba.

No comments:

Post a Comment