
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA na neman wata
kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya na mata 'yan kasa
da shekaru 17.
Hakan ya biyo bayan gazawar da Costa Rica ta yi ne ta kammala aikin ginin filayen wasa a kan lokaci. A da dai an baiwa Costa Rica damar gudanar da gasar ce wadda za a yi a shekara mai zuwa.
FIFA ta ce an yanke shawarar neman wata kasar ce tare da ita Costa Rican saboda matsalolin da suka taso da za su haddasa jinkiri mai tsawo da ba a yi tsammani ba a aikin.
A watan Satumba ne na 2014 ake saran gudanar da gasar ta kasashe 16.
Hukumar ta FIFA ta ce za ta yi nazarin wadanda za su nemi karbar bakuncin gudanar da gasar kafin kwamitin zartarwarta ya yanke shawara a taronta daga ranar 20 zuwa 21 na watan Maris a Zurich.
Costa Rica ta samu damar karbar bakuncin ne a watan Maris na 2011 inda ta yi galaba a kan Ghana da Turkiyya da kuma Uzbekistan.
No comments:
Post a Comment