
'Yan takara a zaben da za'a gudanar a kasar Kenya za
su gudanar da gangamin yakin neman zabensu na karshe,kafin kada kuri'ar
ranar Litinin.
Wannan zai kasance zaben farko da za a gudanar
karkashin sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka tsara domin kaucewa
sake abkuwar mummunan rikicin kabilancin da aka tafka shekaru biyar da
suka gabata.Shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki yayi kira ga 'yan kasar da su gudanar da zaben da za a yi ranar Litinin cikin kwanciyar hankali.
Mr Kibabki dai zai sauka daga mukaminsa bayan wa'adin mulki biyun da yayi.
A tattaunawarsa da BBC daya daga cikin na kan gaba gaba a fafatwar da za a yi a zaben shugaban kasar Firaminista Raila Odinga ya ce zai amince da duk wani sakamakon zaben idan bai samu galaba ba.
Biyu daga cikin 'yan takarar dake kan gaba gaba wato mudaddashen Firaminista, Uhuru Kenyatta da abokin takararsa, William Ruto dai na fuskantar tuhuma daga kotun hukunta aikata masu aikata laifukan yaki ta kasa da kasa, kan zaragin da ake musu da hannu a rikicin da ya faru a baya.
Mutane sama da dubu daya ne suka mutu a rikicn da ya faru a zaben shugaban kasar da aka gudanar a Kanyer cikin shekara ta 2007.
No comments:
Post a Comment