
Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya yi
alkawarin cewa Wayne Rooney zai ci gaba da zama a kulob din har kakar
wasanni mai zuwa.
Dan wasan mai shekaru 27, ba a fara wasan da
United ta yi da Real Madrid a zagaye na biyu na gasar cin kofin zakarun
Turai da shi ba, inda Ferguson ya fara amfani da Danny Welbeck.Wannan ya haifar da rahotonni da dama a jaridun Ingila cewa United za ta sayar da dan wasan a karshen kakar bana.
"Zai kasance tare da mu badi, " a cewar Ferguson. "Na tabbatar muku da wannan."
Ferguson yana magana ne a karon farko tun bayan da aka baiwa Nani jan kati cikin yanayi mai rudani a wasan da United ta sha kashi da 3-2 bayan wasa gida da waje a hannun Real Madrid.
"Wannan ne karo na uku da aka fitar da mu saboda matakin da alkalin wasa ya dauka, abu ne mai matukar wahala amincewa da wannan hukunci," a cewarsa.
Rooney, wanda rahotonni suka ce yana karbar fan 250,000 a kowanne mako a matsayin albashi, ana alakanta shi da komawa kulob daban-daban, cikin harda Paris Saint-Germain.
No comments:
Post a Comment