Shugabannin jam'iyyar islama a Bangladesh, sun yi
kira a yi yajin aikin gama gari don nuna adawa da hukuncin kisan da aka
yankewa daya daga cikin manyan jami'ansu.
An dai zarge su da aikata ta'asa lokacin yakin kwatar 'yanci daga Pakistan a shekarar 1971.Hukumomi sun jibge karin jami'an tsaro gabanin fara yajin aikin.
Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu a wata kwabzawa tsakanin jami'an tsaro da kuma magoya bayan jam'iyyar jama'atu islami tun a ranar alhamis.
Jagoran jam'iyyar 'yan kishin kasa ta Bangladesh Begum Khaleda Zia, ya dora alhakin tashin tashinar akan gwamnati.
Mr Khaleda ya ce dole ne gwamnati ta dakatar da kisan jama'a.Ina gargadin gwamnatin ta daina ko kuma abinda zai biyo baya ba zai kyau ba.
No comments:
Post a Comment