
Tahir gidan yarin da aka sami gawar Ram wanda ake zargi da fyade
Babban wanda ake zargi da yin fyaden taron dangi a birnin Delhi na India an same shi a mace a dakinsa na gidan yari.
Ram Singh, na daya daga cikin samari biyar da
ake zargi da fyade da kuma kisan wata yarinya 'yar makaranta a watan
Disambar bara.Lauyan da yake kare babban wanda ake tuhumar da fyaden ya ce 'yan sanda sun kirashi sun shaida masa cewa wanda yake karewa ya kashe kansa.
Ram Singh, shine matukin motar kirar Bus din da aka yiwa 'yar makarantar kazamin fyaden.
Mutuwar Mr Singh za ta jawowa Hukumomi abin fada wanda tuni suna samun matsin lamba kan shari'ar.
No comments:
Post a Comment