Saturday, 9 March 2013

An sake kwantar da Nelson Mandela a asibiti

Nelson Mandela
An sake kwantar da Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela asibiti saboda abinda jami'ai su ka ce sake duba lafiyar sa , kamar yadda aka tsara
Mai magana da yawun Shugaba Jacob Zuma yace likitoci na duba lafiyar Mandelan game da wa ta laurar da yai fama da ita
Mr Mandela wanda yake da shekaru casa'in da hudu a duniya, ya shafe kusan makonni uku a watan Disambar bara wance a gadon asibiti, bayan da yai fama da cutar huhu.
Ana dai girmama Mandela sosai a nahiyar Afirka

No comments:

Post a Comment