Mataimakin shugaban kasar Venezuela ya bayyana
rasuwar shugaban kasar Hugo Chavez bayan ya yi fama da wata doguwar
rashin lafiya.
Mr Chavez dai bai fito a bainar jama'a ba tun bayan da ya dawo daga Cuba inda aka yi mishin maganin ciwon sankara.Mataimakin shugaban kasar Nicolas Maduro ya bayyana rasuwar shugaban kasar ne cikin kaduwa.
Shugaban kasar mai shekarun haihuwa 58 ya yi fama da matsalar nunfashi ne kafin ya rasu.
No comments:
Post a Comment