
Wata ƙungiyar masu gwagwarmaya da makamai a arewacin
Najeriya mai suna Ansarul muslimina fi biladi sudan tace ta kashe 'yan
ƙasashen waje bakwai da ta sace a watan da ya gabata.
Ƙungiyar ta Ansaru tace ta ɗauki wannan matakin
ne saboda dakarun Najeriya da na Faransan sun kashe musulmi a wani
farmakin da suka kai na ƙoƙarin su na 'yanto waɗanda aka yi garkuwar da
su.Mutanen da aka yi garkuwar da su dai ma'aikata ne na wani kamfanin gine gine mallakar 'yan Lebanon
Uku daga cikin mutanen dai 'yan Labanon ne, sauran hudun kuwa sun fito ne daga ƙasashen Burtaniya, da Girka, da Italiya, da kuma Philippines.
Ana dai tunanin cewa ƙungiyar ta Ansaru, ɓangare ne na ƙungiyar Boko Haram wacce aka yi imanin cewar ita ke riƙe da iyalan Faransawan nan da aka sace a Kamaru.
No comments:
Post a Comment