I received this today from them.
This is to notify you that www.hausawa360.com has been upgraded to www.talkswag.com this is due to upgrade in our service to you.
all recent members that register on www.hausawa360.com can also use their logging credentials to log-on to www.talkswag.com.
swag on members we are working to release our android mobile app for talkswag,
stay online swag on.
C.E.O. Adams
Hausa life and culture
hausa culture,hausa news, hausa movie,hausa music, history of hausa
Saturday, 31 May 2014
Friday, 16 August 2013
hausa chat
we are happy to announce to you the released
of hausawa360.com a social network which operates with to major
languages ENGLISH AND HAUSA it is first of it kind register now and make
new friends, chat, upload pictures/videos/music, of your choice create a fan group for your audience/friends create polls and soo on register now for free on www.hausawa360.com
muna farin cikin gayyatar ku zuwa sabon yanar gizon da muka buda mai amfani da yarurruka 2 wato hausa da turanci(english) a hanzarta ayi rijista a dan zama jerin wanda suka Fara amfani da babbar yanar gizon na farko a duniya ta sada zumuci mai amfani da harshen hausa...........................................mu hadu a can www.hausawa360.com hausawa chat hausa chat room available
muna farin cikin gayyatar ku zuwa sabon yanar gizon da muka buda mai amfani da yarurruka 2 wato hausa da turanci(english) a hanzarta ayi rijista a dan zama jerin wanda suka Fara amfani da babbar yanar gizon na farko a duniya ta sada zumuci mai amfani da harshen hausa...........................................mu hadu a can www.hausawa360.com hausawa chat hausa chat room available
Monday, 11 March 2013
Burkutu ta kashe mutane da dama a Libya
Mutane sama da hamsin ne ake cewa sun mutu daga cikin
daruruwa da aka kwantar a asibitoci a duk fadin Turabulus, babban
birnin kasar Libya, sakamakon shan gurbatacciyar giyar gargajiya wato
burkutu.
Ma'aikatar lafiya ta Libyar ta yi shelar cewa an shiga wani yanayi na ta-baci, a asibitocin kasar.Tun daga ranar Asabar aka fara samun mace macen, kuma adadin ya ci gaba da karuwa.
An gayyato Kamfanonin Dubai zuwa Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta cinma wasu shirye
shirye da wasu kamfanoni a Dubai, wadanda za su je Kanon su saka jari a
harkar da ta shafi sufurin jirgin kasa da zai rika zirga zirga a cikin
birnin Kano.
Baya ga wannan gwamnatin Kanon na tattaunawa da
wasu kamfanonin Dubai domin su zuba jari a bangaren hasken wutar
lantarki da kuma kafa jami'a mai zaman kanta.Gwamna Rabi'u Kwankwaso ya shaidawa cewa a watan gobe su ke sa ran daddalewa kan wadannan batutuwan da mutanen da suka gayyata zuwa Kano.
Jahar Kano dai ta yi fama da matsalolin hare haren 'yan bindiga abinda ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci
Babu shaidar kisan 'yan Setraco - Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce ba a tabbatar da ikirarin
kisan 'yan kasashen waje bakwai, ma'aikatan Setraco da aka kama a jihar
Bauchi ba.
Saboda haka za ta yi iya bakin kokarinta wajen ceto su, da kuma tabbatar da tsaron lafiyarsu.Ministan harkokin wajen kasar, Abba Moro ne ya bayyana hakan.
Inda ya kara da cewa, abin takaici ne yadda al'amarin ya kai ga haka.
Ya ce "Duk da cewa kasashen da ma'aikatan suka fito sun yi amanna an kashe 'yan kasashensu, babu hujjar dake tabbatar da hakan, kuma muna fatan suna raye."
Kungiyar masu fafutukar Islama ta Ansarul Muslimina fi Biladis Sudan ce, ta kame mutanen a watan jiya, a wurin da suke aikin gine-gine a arewacin Najeriya.
Kuma tuni kasashen Birtaniya da Italiya da Girka su ka ce, sun yi amanna an kashe mutanen bakwai a Najeriya, kamar yadda kungiyar Ansaru ta bayyana a wani faifan bidiyon da ta sanya a shafin intanet.
A cewar kungiyar, ta kashe 'yan kasashen Birtaniya da Italiya da Girka da Lebanon da ta yi garkuwa da su ne, saboda yunkurin da dakarun Birtaniya da na Najeriya suka yi na ceto su.
Amma Italiya ta ce babu kamshin gaskiya a wannan batu.
Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, William Hague, ya yi tur da al'amarin.
Wani dansanda ya kashe kansa a india

Tahir gidan yarin da aka sami gawar Ram wanda ake zargi da fyade
Babban wanda ake zargi da yin fyaden taron dangi a birnin Delhi na India an same shi a mace a dakinsa na gidan yari.
Ram Singh, na daya daga cikin samari biyar da
ake zargi da fyade da kuma kisan wata yarinya 'yar makaranta a watan
Disambar bara.Lauyan da yake kare babban wanda ake tuhumar da fyaden ya ce 'yan sanda sun kirashi sun shaida masa cewa wanda yake karewa ya kashe kansa.
Ram Singh, shine matukin motar kirar Bus din da aka yiwa 'yar makarantar kazamin fyaden.
Mutuwar Mr Singh za ta jawowa Hukumomi abin fada wanda tuni suna samun matsin lamba kan shari'ar.
Saturday, 9 March 2013
An sake kwantar da Nelson Mandela a asibiti
An sake kwantar da Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu
Nelson Mandela asibiti saboda abinda jami'ai su ka ce sake duba lafiyar
sa , kamar yadda aka tsara
Mai magana da yawun Shugaba Jacob Zuma yace likitoci na duba lafiyar Mandelan game da wa ta laurar da yai fama da itaMr Mandela wanda yake da shekaru casa'in da hudu a duniya, ya shafe kusan makonni uku a watan Disambar bara wance a gadon asibiti, bayan da yai fama da cutar huhu.
Ana dai girmama Mandela sosai a nahiyar Afirka
Subscribe to:
Comments (Atom)
